Najeriya

An zartar wa wasu mutane hudu hukuncin kisa a Najeriya

Gwamnan Jahar Edo Adam Oshiomhole
Gwamnan Jahar Edo Adam Oshiomhole globalnews

A Najeriya an rataye wasu mutane hudu da aka kama da laifin fashi da makami a Jahar Edo, kuma wannan shi ne hukuncin Kisa na farko da aka samu a Najeriya tun a 2006. Kwamishinan shari’a na Jahar ya tabbatar da zartar da hukuncin.

Talla

Kungiyar Amnesty Internationale, ta bayyana damuwarta kan aiwatar da hukuncin kisan da jami’an Gwamnatin Najeriya suka yi, bayan kotun daukaka kara ta yi watsi da daukaka karar da aka shigar kan hukuncin.

Lucy Freeman, mataimakiyar Daraktan da ke kula da Afrika na kungiyar Amnesty International, ta bayyana cewar idan an tabbatar da aiwatar da hukuncin kisan, zai zama koma wa gidan jiya wajen cin zarafin Bil Adama da aka san Najeriya a baya.

Kotun daukaka kara a Benin, taki amincewa da bukatar wata kungiyar kare hakkin Bil Adama na ganin an jingine hukuncin kisan, wanda tuni Gwamna Adams Oshiomhole ya sanyawa hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI