Afrika ta Kudu

Afrika ta kudu na shirye wajen karbar bakucin Shugaba Obama (Zuma)

Shugaban kasar  Afrika  ta  kudu Jacob Zuma
Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma AFP PHOTO/MUJAHID SAFODIEN

Tun kwantar da shi a gadon Asibiti da aka shiga mako na uku yanzu haka, Shugaban kasar Jacob Zuma ya ziyarci Mandela sau biyu kenan. 

Talla

Jacob Zuma na da karfin guiwar cewa Dattijo Mandela na samun sauki, koda shike wasu bayanan na nuna cewa samun sauki da aka futar ne kawai da baka amma babu sauki.

Dukkan dangi da ‘yan uwan Dattijo Nelson Mandela sun kasance a cikin asibitin yayi da mutan kasar keta adduoi'in  don nema masa sauki.

Ahmed Kathrada mai shekaru 83 yanzu na daga cikin wadanda suka yi zaman shekaru 25 da Dattijo Nelson Mandela a gidan yari.

Shugaban kasar Africa ta Kudu Jacob Zuma ya ce rashin lafiyar Dattijo Nelson Mandela ba zai hana su karban bakuncin Shugaban kasar Amurka Barack Obama ba a tautaunawar sa da  manema labarai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI