Afrika ta Kudu

Al’ummar Afrika ta kudu sun shiga damuwa akan makomar Mandela

Wani yana zana hoton tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela a harabar Asibitin da ya ke jinya a birnin Pretoria
Wani yana zana hoton tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela a harabar Asibitin da ya ke jinya a birnin Pretoria REUTERS/Dylan Martinez

Daruruwan mutane ne suka hada gangamin juyayi a harabar Asibitin da Nelson Mandela ke jinyar rashin lafiyar da aka ruwaito ta tsananta, inda dangi da ‘yan uwa suka shiga cikin damuwa akan makomar tsohon shugaban kasar ta Afrika ta Kudu.

Talla

Mutane da dama ne suka hada gangami suna wake a harabar Asibitin Pretoria Inda ake tsammanin Mandela yana jiran wa’adin shi.

Akwai addu’oi da shugaban Kiristocin Afrika ta kudu ya gudanar domin fatar samun lafiyar Nelson Mandela.

Shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela
Shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela

Tun a ranar 8 ga watan Yuni ne Mandela ke kwance a gadon Asibiti saboda matsalar rashin lafiyar Huhu.

Yanzu haka Shugaban Amurka Barack Obama ya kama hanya zuwa kasar Afrika ta kudu daga Senegal, kuma har yanzu babu wani bayani ko rashin lafiyar Mandela za ta kawo cikas ga muradun ziyarar shugaban na Amurka a kasar.

Nelson Mandela yana cikin shugabannin da aka yi a duniya kuma wanda tarihi ba zai taba mantawa da su saboda girman aikinsa na kawo karshen wariya a kasar Afrika ta kudu.

Mandela shi ne shugaba bakar fata na farko a kasar Afrika ta kudu wanda mutanen kasar ke ado da shi. Shugaban da ya yi aiki wajen tabbatar da zaman lafiya da sansantawa.

Mutanen Afrika ta kudu dai suna ganin Mandela tamkar uba ne a kasarsu.
Nelson Mandela ya kasance kamar wani dango wanda ya daure mutanen kasar a waje daya wajen yakin tabbatar da ‘Yanci.

‘Yan kasar sun yi fatar Mandela zai samu karin shekaru a duniya domin ci gaba da zama jagoran kawo sauyi a tsakanin shugabanninsu Wanda hakan ya sa tsohon shugaban ke shan addu’oi daga al’ummar kasar.

Mandela dai ya kasance wanda ya ceto Afrika ta kudu a lokacin da ta kama hanyar rabewa, Wanda ya kafa sabuwar kasa shekaru 20 da suka gabata.

Tun jawabinsa na Farko a matsayin shugaban kasa a ranar 10 ga watan Mayu shekarar 1994, Siyasar Afrika ta kudu ta canza salo,

Masana suna fatar Jam’iyyar ANC za ta ci gaba da rayuwa karkashin makarantar Mandela wanda duk da kargame shi a gidan yari amma muradun Jam’iyyarsa ne a gaban shi.

A shekarar 1993 ne Nelson Mandela ya karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya tare da shi da shugaba FW de Klerk. Kuma A shekarar 2004 ne Mandela ya bayyana yin ritaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI