Amurka-Afrika

Amnesty ta bukaci a kare hakkokin yan Luwadi da Madugo a Afrika

Wansu  yan luwadi a Afrika
Wansu yan luwadi a Afrika

Kungiyar  Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International, ta bukaci shugaban kasar Amurka, Barack Obama, da yayi anfani da ziyarar sa zuwa nahiyar Afrika, dan kare hakkokin Yan luwadi da madigo. 

Talla

Kungiyar ta zargi wasu kasahsen Afrika, cikin su harda Nigeria da Gambia, da tsaurara dokar wadanda aka samu suna alaka da aikin.Hukumomi  a tarayyar Najeriya sun amince a hukumce zartas da hukuncin daurin shekaru 14 ga Maza masu auren Maza da Mata masu Auren Mata wato ‘yan Luwadi ko Madigo kenan a kasar.

Wannan Dokar da Majalisar Dokoki ta amince da ita dai ta nuna cewar muddin aka kama Maza masu Auren Maza ko Mata masu Auren Mata a dabi’ance ma’ana Ludu ko Madigo, za’a yanke masu hukuncin daurin shekaru 14 cur a gidan Kaso ba tare da wata Magana ba.

Wannan dai ya kara nuna a fili cewar matakin da Majalisun Najeriyar suka dauka a baya na yin fatali da bukatun kasashen yammacin Duniya na amincewa da baiwa ‘yan Ludu da Madigo ‘yancin aurar juna a Najeriya ya kara karfafa kenan.

Yanzu haka dai Rahotanni sun nuna cewar jami’an tsaro a kasar na cigaba da kamen ‘yan Madigo da Luwadi da a halin yanzu ba suda masheda a tarayyar Najeriya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.