MDD-Mali

Dakarun MDD za su karbi ragamar tafiyar da tsaro a Mali

Sansanin 'Yan gudun hijira a Mali
Sansanin 'Yan gudun hijira a Mali Sonia Rolley / RFI

Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta karbi harkar tsaron kasar Mali daga a watan Yuli a yayin da kasar ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa bayan dakarun Faransa sun taimaka wajen kwato yankin Arewaci da ya fada hannun ‘Yan tawaye.

Talla

A ganawar da Majalisar ta yi dangane da rikicin na Mali babu wata Suka da aka samu na yunkurin aikawa da dakarunta zuwa bayan kasar ta fada cikin yaki tun watan Maris na shekarar da ta gabata sanadiyar kwace kusan rabin arewacin kasar da ‘yan Tawaye da kuma kungiyoyin masu kishin lslama suka yi.

Bayan da dakarun Faransa suka kwato yankin Arewaci a halin yanzu dakarun sun dauki haramar mika ragamar harkokin tsaron kasar ga Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin , sai dai akalla sojanta dubu daya ne za su ci gaba da kasancewa domin ci gaba da wanzar da zaman lafiya.

Kimanin Sojojin Majalisar Dinkin Duniya dubu shida ne ke kasar Mali kuma za su dauki nauyin tsaro a lokacin zaben da ake shirin gudanarwa a ranar 28 ga watan Yuli.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.