Najeriya

Sabuwar Jam’iyyar Adawa ta APC ta nada shugabanninta

Gwamnan Jahar Lagos Babatunde Raji Fashola da Jagoran ACN Bola Ahmaed Tinubu da shugaban Jam'iyyar Bisi Akande da Lai Muhammad da Tshon Shugaban Kasa Janar muhammadu Buhari a wajen taron kaddamar da littafin Witness To History na Lai Muhammed a Lagos
Gwamnan Jahar Lagos Babatunde Raji Fashola da Jagoran ACN Bola Ahmaed Tinubu da shugaban Jam'iyyar Bisi Akande da Lai Muhammad da Tshon Shugaban Kasa Janar muhammadu Buhari a wajen taron kaddamar da littafin Witness To History na Lai Muhammed a Lagos primenews

Sabuwar Jam’iyar adawa ta APC da ke neman rajista, ta bayyana shugabaninta na riko, wadanda ake sa ran za su dora ta a tirbar nasara domin kawar da Jam’iyyar PDP da ta kwashe shekaru sama da 10 ta shugabanci a Najeriya.

Talla

Cif Bisi Akande, shi ne shugaban Jam’iyar, Aminu Bello Masari da Annie Okonkwo su ne mataimakansa, Alh Tijani Tumsa shi ne Sakatare, sai kuma Nasir el Rufai a matsayin mataimakinsa.

Hajiya Sadiya ma’aji da Lai Mohammed su ne Sakataren yada labarai, Isa Madu mataimakinsu.

Akwai mataimakan shugabanin shiyoyi da suka hada da Niyi Adebayo da Tom Ikimi da Janar Abdullahi Aboki da Dr Ayim Nyerere da Salisu Fagge da Umaru Duhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI