An samu raguwar cutar Kanjamau a kasashen yammacin Sahara
Wallafawa ranar:
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da cutar kanjamau, tace wasu kasashe Bakwai da ke Yammacin Sahara sun yi nasarar rage sabbin masu kamuwa da cutar da kashi 50, daga shekarar 2009. Kasashen sun hada da Botswana da Habasha da Ghana da Malawi da Namibia daAfrika ta kudu da Zambia.
Shugaban hukumar, Michel Sidibe, yace ganin irin ci gaban da aka samu, akwai alamun cewar, idan an dage ana iya kare kowanne jariri daga kamuwa da cutar.
Sai ya kara da cewar, kasashen da ake samun matsalar yanzu haka sun hada da Najeriya da Angola, inda ake samun karuwar yaran da ke kamuwa da cutar wajen haihuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu