Bakonmu A yau: Sanata Babayo Garba Gamawa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sauti 04:00
Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya ta yi watsi da bukatar shugaba Goodluck Jonathan, na yin gyara ga kasafin kudin kasar na shekarar bana, inda suka bayyana bukatar tasa da cewa ta saba ka’ida.Rashin fahimtar juna tsakanin bangaren majalisa da fadar shugaban kasa, ya zama ruwan dare, yayin da sau da dama wasu ‘yan kasar ke cewa su ba sa gani a kasa, dangane da abin da ya shafi ribar dimukuradiyya.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sanata Babayo Garba Gamawa, ko suna jin abinda talakawa ke fadi kuwa.