Afrika ta Kudu

Mandela ya daina numfashi sai da taimakon na'urar asibiti

Wani yana zana hoton tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela a harabar Asibitin da ya ke jinya a birnin Pretoria
Wani yana zana hoton tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela a harabar Asibitin da ya ke jinya a birnin Pretoria REUTERS/Dylan Martinez

Rahotanni daga Afrika ta Kudu sun ce, tsohon shugaban kasar Nelson Mandela, ya daina numfashi da kansa, sai da taimakon na’urar asibiti, kamar yadda wani dattijo daga cikin ‘yan kabilarsa Napilisi Mandela ya sanar.

Talla

Napilisi ya ce Mandela na cikin mawuyacin hali, kuma babu wani abinda za su iya yi.

Halin da ake ciki a kasar, ya sa shugaba Jacob Zuma ya soke ziyarar da ya shirya kai wa kasar Mozambique.

Yanzu haka ‘yan kasar da dama ne suka yi wa asibitin da Mandela ke kwance kawanya, inda suke gudanar da addu’o’I da kuma nuna damuwarsu dangane da halin da yake ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI