Senegal

Shugaba Obama ya isa kasar Senegal cikin daren da ya gabata

'Yan Senegal na tarben Obama
'Yan Senegal na tarben Obama REUTERS/Joe Penney

Da misalin karfe 8 da miniti 17 na daren jiya ne shugaban kasar Amurka Barack Obama da iyalansa, suka sauka a filin jiragen sama na Leopold Sedar Senghor da ke birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal, domin gudanar da ziyarar aiki har zuwa gobe juma’a a kasar.

Talla

Bayan saukarsa, shugaba Obama ya gaisa da takwaran aikinsa na kasar Senegal Macky Sall, kafin daga bisani ya gaisa da manyan jami’an gwamnatin kasar da suka taru domin tarbensa, yayin da a gefe daya Urgidan shugaban na Amurka da takwrarta ta Senegal suke gaisawa da junansu.

A kan hanyar da ta tashi daga filin saukar jiragen sama zuwa tsakiyar birnin Dakar, a duk inda ka duba, tutar kasar Senegal da ta Amurka ce ke kadawa, yayin da dubban mutane suka yi cincirindo a gefen hanya domin yi masa marhabin.

Kamar dai yadda aka saba a duk lokacin da wani muhimmin bako ke gudanar da ziyara a wata kasa ta nahiyar Afirka, ko a kasar Senegal hukumomi sun dauki muhimman matakan tsaro, kuma ana gudanar da wannan aiki ne a matsayin hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaron kasar da takwarorinsu na Amurka.

A safiyar yau alhamis kuwa, an shirya ganawa ta musamman ne tsakanin shugaba Obama da mai masaukinsa Sall a fadar shugaban kasar, kafin daga bisani su gabatar taron manema labarai na hadin gwiwa.

Daga nan kuma Obama zai wuce zuwa Kotun Kolin kasar da kuma tsibirin Gore, da ya shiga sahun tarihin duniya sakamakon kasancewarsa wani sansanin tattara bayi da kuma jigilarsu zuwa Turai da Amurka a shekarun da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI