Masar

Shugaban Masar ya ce kasar ta doshi hanyar durkushewa

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi
Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi, ya yi gargadin cewar kasar ta kama hanyar durkushewa, saboda rikicin siyasar da ya dabaibaye ta, bayan wani tashin hankalin da ya hallaka ran mutum guda, ya kuma raunana sama da 200.

Talla

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar ta talabijin dan cika shekara guda da hawa karagar mulki, shugaba Morsi ya ce bambancin da ake samu a kasar, ya kai wani mataki na yi wa demokradiya barazana.

A zanga-zangar da aka gudanar a jiya laraba, magoya bayan bangarorin biyu sun yi arangama da junansu, inda akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa, yayin da wasu da aka ce yawansu ya haura 200 suka samu raunuka.

Zanga-zangar ta jiya, wadda ta wakkana a lardin Mansoura da ke gabar kogin Nilo a arewacin kasarta Masar, ta kazance ne bayan da magoya bayan ‘yan adawa suka afkawa magoya bayan shugaban kasar Mohd Morsi, da ke gudanar da gangami domin jaddada goyon bayan ga shugabansu.

Su dai ‘yan hamayya, na nuna adawarsu ne da abin da suka kira bambancin da shugaban Morsi ke nunawa tsakanin al’ummar kasar, inda wasu ke cewa ya karkata akalar nasarar juyin juya halin da al’ummar kasar suka samar, inda a maimakon ya amfani al’umma, sai ya kasance Morsi da magoya bayansa ne kawai ke amfana da shi a cewarsu.

Tuni dai magoya bayan wani gungu na ‘yan adawa mai kiran kansa da suna Tamarod, wato Tawaye da harshen Larabci, ya ce ya tattara sa hannun mutane milyan 15, wadanda ke neman a sake gudanar da zaben shugaban kasa, lamarin da ke iya sake jefa kasar a cikin wani yanayi na tashe-tashen hankula.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI