Masar

Zanga-zangar adawa da gwamnatin Morsi na Masar

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Morsi na Masar.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Morsi na Masar. REUTERSAsmaa Waguih

‘Yan adawa a kasar Masar sun shirya gudanar da zanga-zangar gama gari domin adawa da gwamnatin Demokuradiya ta shugaba Muhammed Morsi a dai dai lokacin da gwamnatinsa ke  bukin cika shekara bayan kaddamar da zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane uku cikinsu har da Ba’amurke.

Talla

Gwamnatin Amurka ta gargadi Amurkawa su kauracewa kasar Masar saboda fargabar barkewar rikici tsakanin magoya bayan gwamnatin Musulunci ta shugaba Morsi da kuma ‘Yan adawa masu ra’ayin ganin an kafa gwamnatin ‘Yan Boko zalla a kasar.

Masu zanga-zangar sun ce Morsi ya sabawa nasarar da suka samu a juyin juya halin da suka gudanar a shekarar 2011 wanda ya kawo karshen mulkin shekaru sama da 30 na Hosni Mubarak.

Kasashen Birtaniya da Faransa sun yi kira ga ‘Yan kasarsu su kaurace wa shiga cikin masu zanga-zangar ko wani taro na yawan mutane don gudun kada tsautsayi ya rutsa da su.

A ranar Lahadi, ‘Yan adawar Masar sun yi kiran gudanar da babbar zanga-zanga domin neman lalle sai Morsi ya yi murabus amma a daya bangaren akwai zanga-zangar mayar da martani daga magoya bayan Morsi na jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Brotherhood da suka shirya.

Masana dai suna ganin idan har ba a dauki mataki ba, rikicin siyasar Masar na iya jefa kasar cikin yakin basasa.

Yawancin kanun labaran Jaridun Masar ,suna nuni ne da Masar ta dare zuwa guda biyu.

A ranar juma’a an kashe wani dan kasar Amurka Andrew Pochter, da ke aikin daukar hoton zanga-zanga a birnin Alexandria.

Ana ganin masu adawa da Morsi, mafi yawancinsu wadanda suka yi adawa da shi ne a lokacin zaben shugaban kasa.

A lokacin da ya ke jawabi ga ‘Yan kasa a kafar Telebijin, Shugaba Morsi ya yi gargadin cewar rikicin zai gurgunta ci gaban Masar tare da kira ga ‘Yan adawa su zo a zauna teburin sasantawa. Daga bisani ‘Yan adawa sun fito sun yi wasti da kiran shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI