Masar

Morsi ya yi watsi da wa’adin Sojojin Masar

Masu adawa da gwamnatin Morsi a dandallin Tahrir, a birnin Al kahira
Masu adawa da gwamnatin Morsi a dandallin Tahrir, a birnin Al kahira REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Shugaban Kasar Masar, Mohamed Morsi ya yi watsi da wa’adin da rundunar sojin kasar ta ba shi, na warware rikicin siyasar kasar cikin sa’oi 48 idan har shugaban bai amsa kiran ‘Yan kasa ba. Shugaba Morsi yace zai ci gaba da shirinsa na sasanta bangarorin siyasar kasar, inda ya bayyana matakin sojin a matsayin yunkurin juyin mulki.

Talla

A jawabin na Sojojin a kafar Talabijin din Masar, sun ce Kasar tana cikin rudani bayan Miliyoyan ‘Yan kasar sun fito saman tituna domin adawa da gwamnatin Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta shugaba Morsi.

“Idan ba a cim ma bukatun Jama’a ba a wa’adin da muka diba, za mu dauki mataki” a cewar Babban hafsan Sojan Masar Janar Abdel Fattah al-Sisi.

Amma a sakon martani, fadar Shugaba Morsi tace za ta ci gaba da kokarinta na neman sasantawa.

Tuni dai ‘Yan adawa suka ba Shugaba Mrosi wa’adin sa’ao’I 24 da ya yi murabus. Kuma ikirarin na Sojin kasar ya kara farantawa ‘Yan adawar rai, amma magoya bayan shugaba Morsi suna ganin kamar Sojin kasar suna kokarin yin juyin mulki ne saboda sun linka yawan ‘Yan adawan.

Yanzu haka Ministocin Morsi kusan Biyar ne suka yi murabus cikinsu kuma har da Ministan harkokin waje, Mohammed Kamel Amr, da ministocin Muhalli da Sadarwa. Kamfanin Dillancin labaran kasar ta MENA, yace Ministan harakokin Wajen Masar shi ne babban jami’I na baya bayan nan da ya sauka daga mukaminsa.

Masar dai yanzu ta rabu gida biyu tsakanin magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi da kuma bangaren ‘Yan adawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan abinda zanga zangar kasar Masar zai haifar ga sauran kasashen da ke Gabas ta Tsakiya. Mataimakin mai Magana da yawun kakakin Majalisar, Eduardo del Buey, yace duniya na kallon abin da ke faruwa a Masar, kuma matakin da kasar ta dauka, zai shafi Yankin baki daya.

Kakakin Majalisar yace, tattaunawa da kuma kaucewa tashin hankali sune hanyoyin warware duk wani rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.