Zimbabwe

Zimbabwe ta yi barazanar ficewa daga kungiyar kasashen kudancin Africa

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe Reuters/Philimon Bulwayo

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yayi gargadin cewa kasar sa na iya ficewa daga kungiyar hada kan kasashen kudancin Africa, mai kasashen 15.Shugaba Robert Mugabe wanda yake fadin haka a jawabindsa wajen laccar kaddamar da yakin neman zaben shi, yace babu shakka Zimbabwe na iya ficewa da kungiyar don radin kanta.A cewar sa muddin yaga kungiyar zata yi abin da bai dace ba, to kuwa kasar sa zata fice.Kungiyar kasashen kudancin Africa dai sun dage da cewa zasu yi kafar ungula gameda bukatar shugaba Mugabe na neman a jinkirta zaben kasar.