Zimbabwe

Tsvangirai ya nuna damuwarsa game da rashin aiwatar da sauye sauye kamin zabe

Firaministan kasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai a lokacin yakin neman zabe
Firaministan kasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai a lokacin yakin neman zabe REUTERS/Philimon Bulawayo

Firministan kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, ya bayyana damuwar sa kan rashin aiwatar da sauye sauye, kafin zaben shugaban kasar da za’a gudanar a ranar 31 ga watan nan. 

Talla

Yayin da yake kaddamar day akin neman zaben sa a Marondera, Tsvangirai yacem babu wani sauyi da aka samu na gudanar da ayyukan jarida da kuma tabbatar da gudanar da karbaben zabe.

Kotun kolin kasar a makon jiya, tayi watsi da bukatar dage zaben, kamar yadda Fira Ministan da kungiyar kasashen dake kudancin Afrika suka nemi ayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.