Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu ta cika shekara Biyu da samun ‘Yanci

'Yan kasar Sudan ta kudu suna murnar samun 'Yanci a ranar 9 ga watan Juli
'Yan kasar Sudan ta kudu suna murnar samun 'Yanci a ranar 9 ga watan Juli IRIN/Jose Miguel Calatayud

A ranar 9 ga watan Juli ne kasar Sudan ta kudu ke bikin cika shekaru Biyu da samun ‘Yancin kai bayan ballewa daga Sudan. A watan Janairun shekarar 2011 ‘Yan kudancin Sudan, suka kada kuri’ar amincewa da ballewa, lamarin da ya ba kasar zama ‘yar auta tsakanin kasashen duniya.

Talla

Bayan samun ‘yancin kai Sudan ta Kudu ta kasance mamba ta 193, a Majalisar Dinkin Duniya, kuma kasa ta 54 a kungiyar hadin kan Nahiyar Africa ta AU.

Samun ‘Yanci  ya kasance abin farin ciki ga al’ummar yankin bayan sun kada kuri’ar ballewa daga Sudan. Yawancin mutanen Sudan ta Kudu sun yi imanin samun ‘Yancinsu zai taimaka  wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gabansu bayan kwashe shekaru ana tabka yaki.

Amma har yanzu akwai takun saka tsakanin Sudan ta kudu da makwabciyarta, ta Arewa akan rikicin iyakokinsu masu arzikin Man fetir, lamarin da ke ci gaba da yin illa ga tattalin arzikin kasashen biyu.

A watan Satumba na bara kasashen Sudan ta kudu da Sudan sun cim ma wata yarjejeniya a Addis Ababa da ta shafi tsaron kan iyakokinsu da arzikin Mai, a matsayin wani mataki da ake ganin kasashen sun dauka domin warware rikicin da ke tsakaninsu.

Masu lura da lamura na ganin Sudan ta Kudu na kan matakan tsayawa da kafafunta, a dai dai lokacin da take kokarin samun kawance a ciki da wajen Nahiyar Africa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.