Mali

Romano Prodi ya nuna shakku game da yadda ake shirya wa zaben Mali

Romano Prodi, manzo Majalisar Dinkin Duniya a Sahel
Romano Prodi, manzo Majalisar Dinkin Duniya a Sahel REUTERS/Stringer

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Yankin Sahel, Romano Prodi, ya bayyana fargabarsa kan shirin zaben kasar Mali, da kuma yadda za’a bai wa ‘yan gudun hijira damar kada kuri’unsu.

Talla

Prodi wanda ya bayyana zaben a matsayin matakin farko na mayar da kasar kan turbar dimokuradiyya, ya ce akwai kalubale sosai da ke tattare da yakin neman zaben.

A yau alhamis ne ake kyautata zaton cewa kantoman mulki daga birnin Bamako zai isa birnin Kidal da ke arewacin kasar domin soma shirya wa zaben, kuma zai kasance babban jami’in gwamnati na farko da zai isa birnin tun daga lokacin da ‘yan tawaye suka kwace shi daga hannun sojojin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.