Masar
Ana Shirin Tagwayen Bore A Kasar Masar
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yau juma’a ta farkon watan Ramadan, al’ummar kasar Masar na cikin fargaba, dangane da yiyuwar samun arangama tsakanin magoyan bayan tubabben shugaban kasar Mohammed Morsi da shi.Wannan na zuwa ne a daidai wani lokaci da kasashen duniya ke yin kira ga al’ummar kasar da su kai zuciya nesa. Karon farko tun bayan kifar da mahaifinsa daga karagar mulki, daya daga cikin ‘yaya tubabben shugaba Mohammad Morsi, wato Osama Morsi ya yi magana da manema labarai, inda yake cewa ya nemi ganin mahaifin sa amma kuma an hana shi.