Najeriya

Boko Haram ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar  da ake kira Boko Haram a Najeriya tare da wasu Mambobin kungiyar
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar da ake kira Boko Haram a Najeriya tare da wasu Mambobin kungiyar AFP PHOTO / YOUTUBE

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Jama’tu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad da ake wa lakabi da Boko Haram, ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta da Gwamnatin Nigeria tace ta kulla da kungiyar. Shugaban kungiyar yace babu wani wakili day a tura domin tattaunawa da Gwamnati.

Talla

Shekau yace suna goyon bayan harin da ‘Yan bindiga suka kai a makarantar Mamudo a Jahar Yobe wanda ya kashe yara kimanin 42. Amma kungiyar ba ta dauki alhakin kai harin ba, A wani Sakon Bidiyo na tsawon Mintina 10.

“Muna goyon bayan harin da aka kai a Makarantar Boko ta Mamudo” inji Shekau.
An aikawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa ne da sakon Bidiyon, wanda ke dauke da bayanin Imam Abubakar Shekaru wanda Amurka ta jefa sunansa cikin jerin sunayen ‘Yan ta’adda a duniya.

Shedun gani da ido sun ce da safiyar safiya ne ‘Yan bindiga suka kai hari a Makarantar Mamudo a Jahar Yobe, inda suka yi wa daliban makarantar kawanya kafin su jefa bama bamai tare da bude wuta.

Yawancin wadanda suka mutu a harin yara ne dalibai.

A cikin sakon Bidiyon, Shekau ya kyamaci makarantun Boko wanda ya danganta a matsayin sun sabawa addinin Islama. Sai dai bai fito ya yi ikirarin daukar alhakin kai harin ba.

Jahar Yobe dai tana cikin jahohi uku a arewacin Najeriya da aka kafawa dokar ta-baci a watan Mayu domin farautar maakan Kungiyar Boko Haram.

A cikin mako, shugaban kwamitin sasantawa da kungiyar Boko Haram, Tanimu Turaki ya yi ikirarin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tare da shi da wani da ya kira kan shi mataimakin Shekau.

Amma Shekau ya karyata matakin na cim ma yarjejeniyar.

“Mu ba mu san Kabiru Turaki ba, kuma ba mu taba magana da shi ba, karya ya ke yi. Inji Shekau.

Imam Shekau yace za su ci gaba da gwagwarmaya har sai sun kafa gwamnatin Musulunci a Najeriya.

A watan Yuni, Gwamnatin Amurka ta zuba kudi Dala Miliyan 7 ga duk wanda ya taimaka aka cafke Shakau.

Rikicin Boko Haram ya janyo hasarar rayukan mutane kimanin 3,600, tun da suka kaddamar da yakin mayar da martanin kisan Shugabansu Muhammad Yusuf a shekarar 2009.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.