Rwanda-ICC-Congo

Rwanda ta zargi Sojan Majalisar Dinkin Duniya da hada baki da 'yan tawayen Hutu

Paul Kagame, shugaban Rwanda.
Paul Kagame, shugaban Rwanda. REUTERS/Gus Ruelas

Kasar Rwanda ta zargi sabuwar rundunar Majalisar Dinkin Duniya da ke farautar ‘yan tawayen M 23 da hada kai da ‘yan tawayen Hutu da ake zargi da kisan kare dangi shekarar 1994, matakin dake barazana ga zaman lafiyar yankin.

Talla

Jakadiyar Rwanda a Majalisar Dinkin Duniya, Eugene Richard Gasana, a wasikar da ta mikawa shugabar Majalisar ta wannan wata, Rosemary Di Carlo ta Amurka, ta ce kwamandojin Majalisar Dinkin Duniya sun gana da ‘yan tawayen FDLR da suka rage daga cikin ‘yan tawayen Hutu, kuma hakan na iya haifar da tashin hankali a Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.