Kamaru

An kashe wani da ke fafutikar kare ‘Yan Luwadi a Kamaru

Eric Ohena Lembembe, wani fitaccen mai fafutikar kare hakkin ‘Yan luwadi a kasar Kamaru
Eric Ohena Lembembe, wani fitaccen mai fafutikar kare hakkin ‘Yan luwadi a kasar Kamaru AP Photo/Erasing via leader post

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tace an hallaka wani fitaccen mai fafutikar kare hakkin ‘Yan luwadi a kasar Kamaru, Eric Lembembe a birnin Yaounde. Kungiyar tace, an karya wuya da kafar Lembembe, yayin da aka kona fuskarsa da hannayensa.

Talla

Kungiyar tace, zuwa yanzu ba a san wadanda suka aikata kisan ba.

Aikata Luwadi da Madigo dai abu ne da al’ummar Kamaru suke la’anta.

Amma kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch ta bukaci gwamnati ta tashi tsaye domin gano wadanda suka aikata kisan.

Lembembe, ya dade yana fatawar kare ‘Yan Luwadi a Kamaru duk da la’antar al’amarin, Abokanansa ne suka gano gawar shi a Yaounde a ranar Litinin bayan shafe kwanaki suna neman shi a waya ba su same shi ba.

Kasashen Amurka da Turai sun yi barazanar katse ba kasar Kamaru tallafi saboda yin fatali da dokar kare ‘Yan Luwadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.