Guinea

An tsinci gawawwakin mutane 54 bayan fadan kabilancin da ya barke a Guinea

Tashin hankalin kasar Guinea
Tashin hankalin kasar Guinea Reuters

Jami’an aikin kiwon lafiya a kasar Guinea, sun ce sun samu gawawwakin mutane 54 bayan fadan kabilancin da aka yi a cikin kasar.  

Talla

Hukumomin sun ce, za su mika gawawakin ga ‘yan uwan mutanen daga cikin kabilun biyu, dan yi masu jana’iza.

Idan dai ba’ amanta ba, an samu barkewar tashin hankali tsakanin kabilar Guerze da Konianke, abinda ya kaiga rasa rayukan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.