Zimbabwe

Zimbabwe ta zargi Amurka da mata katsalandan

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe Reuters/Philimon Bulawayo

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya bayyana Amurka a matsayin kasa ta maras hankali sakamakon zargin da Amurkar ta yi na cewa akwai kura-kurai a zaben da ake shirin gudanarwa a Zimbabwe. Mugabe, wanda ke gabatar da jawabi a gaban dubban magoya bayansa, ya ce Amurka na bukatar Zimbabwe ta gudanar da zabenta ba tare da ta aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata ba, ai wannan alamar tabin hankali ce.