Mali

An sako jami’an zabe Hudu [4] da mataimakin magajin garin, da ‘yan bindiga suka sace a Mali.

Dakarun kasar Congo
Dakarun kasar Congo RFI

An dai sako wadannan mutanen jami’an zabe ne da aka kama a garin Tessalit, da ke arewacin kasar Mali, bayan da masu garkuwa da su suka gudanar da wata tattaunawa da jami’an kasar ta Mali.

Talla

Sace mutanen, da ke zuwa mako daya kafin zaben shugaban kasar, ya nuna yiwuwar matsalar tsaro, a lokacin zaben da ake fatan zai shata layi tsakanin juyin mulki da tashin tashina daga ‘yan bindiga masu tsanain kishin Islama.

Sai dai wasu na ganin zaben zai iya tunzura ‘yan kasar su sake daukar makamai, sakamakn rashin shiri yadda ya kamata.

Mutane Shida dai sun je ne a babban Dakin Taro na Tessalit, wani dan Gari dake a lungu, da nisan Kilomitoci 200 Arewacin birnin Kidal domin su shirya yanda za’a rarraba Katin shaida ta masu zabe da sukayi Rajista, lokacin da aka kama su.

Jami’ai a Kidal sun bayyana cewar an kama Mamban masu rinjaye na ‘yan tawayen MNLA ne bisa zargin cewar shi ne ya bada damar a yi garkuwa da wadannan mutane

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.