Cote d'Ivoire

Mutane uku ne suka rasu a wani gidan yarin Abidjan

Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Bagbo lokacin da ka kama shi
Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Bagbo lokacin da ka kama shi AFP/TCI

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a marecen jiya, lokacin da fursunoni suka yi kokarin tserewa daga wani gidan yari da ake tsare da su a birnin Abidjan fadar gwamnatin kasar Cote D’Ivoire.

Talla

Rahotanni sun ce da dama daga cikin wadanda ake tsare da su a wannan gidan yari, magoya bayan tsohon shugaban kasar ne Laurent Bagbo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.