Nijar

An cafke wasu jami'an tsaro a Nijar bisa zargin shiryawa kasa makarkashiya

Shugaban kasar Nijar Issifou Mahamadou cikin sojoji lokacin da ya ziyarci garin Agadez
Shugaban kasar Nijar Issifou Mahamadou cikin sojoji lokacin da ya ziyarci garin Agadez RFI/Sonia Rolley

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa, an kama wasu jami’an tsaro da dama da ake zargi da yunkurin yi wa kasar zagon kasa. 

Talla

Baynan sun ce, ana can ana gudanar da bincike kan wadanda ake zargin, duk da yake hukumomin kasar sun ki yin karin haske dangane da lamarin.

Ko a cikin shekarar da ta gabata dai shugaban kasar da kansa Issifou Mahamadou wanda ke gabatar da jawabi dangane da cikar kasar shekaru 52 da samun ‘yancin kai, ya fito fili inda ya ce an cafke wasu sojoji da ke yunkurin hallaka shi, to sai dai daga bisani kotu ta bayar da umurnin sakin sojojin saboda rashin kwararan hujjoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.