Nigeria

Kamfanin Dangote na shirin gina matatar mai da kamfanin sarrafa taki

Aliku Dangote
Aliku Dangote

Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya sanar da shirin gina katafariyar matatar man fetur a Najeriya, tare da kamfanin yin takin zamani wanda zai ci kudi Dala biliyan 9, don rage dogaron shigar da tacaccen mai a kasar.

Talla

Sanarwar da kamfanin ya bayar, ta nuna cewar, kamfanin ya kulla yarjejeniya da wasu bankuna na samun rancen Dala biliyan kusan uku da rabi na gina matatar man, wadda ake saran zai samar da ayyukan yi 9,500 da kuma samar wa ‘yan kasuwa sama da 25,000 abinda za su yi.

Ana saran kammala gina matatar a kudu maso Yammacin Nigeria cikin shekaru 3 zuwa 4.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.