Isa ga babban shafi
Madagascar-AU

AU ta dage takunkumi da ta kakabawa shugaban kasar Madagasacar

Reuters
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Kungiyar Tarayyar kasashen Afrika ta AU ta dage takunkumin da ta kakabawa shugaban kasar Madagasacar, Andry Rajoelina, cikin har da takunkumi  haramta mai kudaden ajiyarshi a bankuna.

Talla

A cewar rahotanni, an dage takunkuman ne saboda yunkurin da kasar ke yi na komawa kan turbar demokradiya bayan an saka ranar 25 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a yi zabe.
A watan maris din shekarar da ta gabata ne aka kakabawa shugaban takunkuman bayan ya hambarar da gwamnatin kasar da taimakon dakarunta, lamarin da ya jawo koma baya ga shirin gudanar da zaben shugaban kasa da ake yunkurin yi a lokacin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.