Somalia-UE

Tallafin Hukumar Nahiyar Turey zuwa kasar Somalia

Hassan Sheick Mohamud, Shugaban kasar Somalia
Hassan Sheick Mohamud, Shugaban kasar Somalia

Kwamishinan Hukumar kula da yankin Nahiyar Turai Jose Manuel Barrosa ya ce sun shirya samar da akalla Euro Billiyan 1.8 ga kasar ta Somaliya.

Talla

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya sanar da matsayar da aka cimma da masu bada tallafi na kasa-da-kasa dangane da alwashin samar da kusan Euro Billiyan 2 a matsayin taimako zuwa kasar Somaliya.

Yace Euro Billiyan 1.8 makudan kudi ne, kuma Somaliya zata yi wawan Kamu, lura da cewar kasar na kokarin farfado da kanta daga durkushewar tattalin arziki da ta samun kanta a cikin.

Manuel Boroso ya bayyana cewar kungiyar tarayyar Turai za ta baiwa kasar karin Euro Milliyan 650 kari ga Euro Billiyan 1.2.

Wannan dai shi ya nuna cewar akwai saura tsakanin kungiyar ta tarayyar Turai da Somaliya, amma har yanzu akwai sauran rina a kaba, a fani tsaro, da kare ‘yancin bil’adama.

Kari ga hakkan kasar Birtaniya ma ta bada tallafin Founds Milliyan 50 ga kasar ta Somaliya domin tallafawa bangaren lafiya da tattalin arziki, a yayin da Jamus ta bada Euro Milliyan 90, Sweden ta zuba nata Milliyan 170 na kudin Euro, kasar Denmark kuma ta ce zata bada Dollar Miliyan 124.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.