Madagascar-EU

Kungiyar EU zata aike da masu sa ido a zaben kasar Madagaskar

Shugaban kasar Madagascar, Andry Rajoelina
Shugaban kasar Madagascar, Andry Rajoelina Reuters

Wani jakadan kungiyar tarayyar Turai a Antananarivo Leonidas Tezapsidis, ya bayyana cewar kungiyar na shirin aika masu sa Ido 100 a zaben shugaban kasar Madagascar.A Makon Gobe ne ake sa Ran isar Tawagar farko ta masu sa Idon, sauran kuma sai a karshen Wata.Za‘a dai gudanar da zaben shugaban kasa a tsibirin na Madagascar mai yawan mutane akalla Miliyan 22 ne a ran 25 ga Watan Okotoba.Kasar Madagascar dai ta fada cikin tashin hankali ne, tun bayan da sanannen Mawakin nan kuma Magajin garin Antananaribo Andry Rajoelina ya kifar da gwamnatin Marc Ravalomanana a wani juyin mulkin da ya samu goyon bayan Sojojin kasar, shekaru 4 da suka gabata.Tun lokacin ne dai kasar ta fada cikin tsananin tashin hankalin Siyasa daya gurgunta tattalin arzikinta, ya kuma jefa dubban Mutane cikin kangin tsananain Talauci.Bayan kamala zaben shugaban kasar dai, za’a kuma gudanar da na ‘yan Majalisu a ran 20 ga Watan Disamba.An cimma matsayar gudanar da zabubbukan ne, bayan da aka yita shata lokaci ana dagewa sakamakon rashin kudi da takun saka tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar.