Kenya

Mutane 30 sun mutu a harin ‘yan Bindiga a Nairobin kasar Kenya

harin kasar Kenya
harin kasar Kenya nydailynews.com

Akalla mutane 30 ne aka tabbatar da cewar sun mutu, wasu da dama da suka kai 60 suka jikkata a wani harin da ‘yan Bindiga suka kai a wata karamar Kasuwa dake a babban Birni Nirobin kasar Kenya.

Talla

Wani dan Sanda dai ya bayyana cewar a kusa da karamar Kasuwar, an samu akalla Gawawwaki 13 yashe a wrare daban daban, sai dai a cewar sa, ‘yan Uwan sa dake a saman Benen Kasuwar sun bayyana masa cewar akwai Karin Gawawwaki.

Jami’an kungiyar Red Cross a Nirobin Kenya sun bayyana cewar mutane Gwammai ne aka raunata, sun kuma bayyana bukatar a taimaka masu da Jini domin mutanen da suka raunata na bukata ainun.

Yanzu haka dai an bayyana kara kai Jami’an Soji a harabar wurin da abin ya auku, domin inganta tsaro.

Da farko dai an bada labarin cewar Maharan da suka afkawa Kasuwar sun zo ne cikin shigar Burtu suka kuma shiga luguden Wuta har suka kashe mutane 20.

Akwai ma Rahotannin dake cewar ‘yan Bindigar na Magana ne da harshen Larabci dana Somali a wannan harin da aka bayyana a matsayin mafi muni tun bayan wanda aka zargi kungiyar al-Qaeda da kaiwa a ofishin Jakadancin Majalisar dunkin Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.