Sudan-Birtaniya

Birtaniya ta nemi Sudan ta yi taka tsan-tsan

Masu Zanga-Zanga a kasar Sudan
Masu Zanga-Zanga a kasar Sudan

Kasar Britaniya ta bukaci Sudan da ta yi taka tsan-tsan akan zanga zangar da ake yi a cikin kasar ta karin farashin man fetur, wajen bude hanyar tattaunawa don warware matsalar ta hanyar siyasa. Mataimakin Sakataren harkokin wajen kasar, Simon Frasier, ya ce suna fatar zanga-zangar zata sanya gwamnati nazari kan bukatun jama’a da kuma fatar magancesu.

Talla

Gwamnatin kasar tace mutane 34 suka mutu a arangamar da masu zanga zangar suka yi da ‘Yan Sanda, adadin da kungiyoyin fararen hula suka ce ya ribanya haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI