Amurka

Jam’iyyar Obama ta lashe zabe a New York da Virginia

Dan takara  Bill de Blasio  tare da matarsa da 'yaya suna murnar lashe zabe a New York
Dan takara Bill de Blasio tare da matarsa da 'yaya suna murnar lashe zabe a New York REUTERS/Carlo Allegri

Jam’iyyar Democrat me mulki a Amurka ta lashe zaben gwamnoni da aka yi a Jahohin New York City da Virginia, wanda shi ne zabe na farko da aka gudanar bayan sake zaben shugaba Barack Obama a 2012.

Talla

Dan takara Bill de Blasio na Democrat shi ne ya lashe zaben da aka gudanar kuma wanda zai gaji Michael Bloomberg.

A Virginia kuma Dan takarar Republican mai adawa Ken Cuccinelli ya sha kaye ne a hannun Terry McAuliffe na Democrat. Amma a New Jersey an sake zaben Chris Christie ne a matsayin gwamnan Jahar.

Wannan zaben na gwamnnoni da ake gudanarwa kamar wani zakaran gwajin dafi ne tsakanin Jam’iyyun na Amurka guda biyu kafin a gudanar da zaben ‘Yan Majalisu a badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.