Afrika ta Kudu

Tutu ya nemi kasashen renon Ingila su kauracewa taron Sri Lanka

Desmond Tutu na kasar Afrika ta Kudu
Desmond Tutu na kasar Afrika ta Kudu REUTERS/Mark Wessels

Shahrarren mai fafutar kare hakkin bil’adama a kasar Afirka ta Kudu, Archibishop Desmond Tutu, ya ce kamata ya yi shugabannin kasashen Renon Ingila, su kaurace taron kungiyar Commonwealth da aka shirya gudanarwa a kasar Sri Lanka domin tilasta wa hukumomin kasar hukunta masu hannu wajen aikata laifufukan yaki a kasar.

Talla

Tutu ya zargi gwamnatin kasar ta Sri Lanka da kin karba kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi ma ta domin gudanar da bincike dangane zargin kisa da kuma zarafin dan adam a lokacin da aka kaddamar da yakin murkushe kungiyar Tamil Tigers a shekara ta 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.