Masar

Masar za ta bunkasa dangantakar ta da Rasha

Shugaban rikon kwaryar kasar Masar adly Mansuour (tsakiya) yana gaisawa da mutanen Masar
Shugaban rikon kwaryar kasar Masar adly Mansuour (tsakiya) yana gaisawa da mutanen Masar REUTERS/SPA/Handout via Reuters

Kasar Masar ta dauki matakin bunkasa dangantakar dake tsakanin ta da Rasha, sakamakon matsalar da suka samu da kawar ta Amurka. 

Talla

Ministan harkokin wajen kasar, Nabil Fahmy ya bayyana haka, kafin ziyarar minitocin tsaro da harkokin wajen Rasha a birnin Alkahira jibi laraba.

Dangantakar kasshen biyu ta dan yi tsami kan yadda soji suka murkushe magoya bayan hambararen shugaban kasa Mohammed Morsi, abinda ya sa kasar ta dakatar da baiwa Masar makamai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.