Kenya

An fara kokarin ceto mutanen kauyen da 'yan bindiga suka mamaye a Kenya

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta Reuters/Noor Khamis

‘Yan Sanda a kasar Kenya sun kaddamar da aikin ceto mutanen wani kauye da Yan bindiga suka mamaye sakamakon rikicin iyaka.Hukumar agajin gaggawa ta kasar, tace wasu ‘yan bindiga ne suka mamaye garin Lorokon, inda ake tashin hankali tsakanin ‘Yan kabilar Pokot da makwabtan su Turkana, wadanda suka kwace tashoshin ‘Yan Sanda guda uku a yankin.Lamarin ya biyo bayan takaddamar da al’ummomin 2 ke yi kan mallakin iyakoki, kuma kokarin da ‘yan sanda ke yi na kwato ofisoshin ya gamu da turhjiya daga sojan sa kan.Tuni aka kafa dokar hana fitar dare a Ynakin.