Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta amince da dokar haramta zanga zanga

Shugaban kasar Masar, Adly Mansour
Shugaban kasar Masar, Adly Mansour Reuters
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed

Shugaban Kasar Masar, Adley Mansour, ya amince da wata dokar da zata haramta gudanar da zanga zanga a kasar. Wannan na zuwa ne kwanaki kadan, bayan kawo karshen dokar ta bacin watanni uku da sojoji suka sa.Kakakin fadar shugaban, Ehab Badawi, yace dokar zata kare masu gudanar da zanga zanga ne, ba wai hana su gaba daya ba.Kungiyoyin fararen hula sun soki dokar wadda ta kunshi sanar da hukumomi kwanaki kafin duk wata zanga zanga da zasu yi. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.