Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Faransa za ta tura karin sojoji zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Faransa ta amince ta tura karin sojoji zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wadanda yawansu zai kai dubu daya don tabbattar da zaman lafiya a kasar da ke gap da fadawa cikin yakin basasa.
Talla
Fira Ministan ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Nicolas Tiangaye, bayan tattaunawa da takwaransa na Faransa Jean-Marc Ayrault a Paris, ya ce ana sa-ran isar sojojin birnin Bangui da zarar Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shirin a makon gobe.
Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Jan Eliason, ya ce halin tsaro ya tabarbare a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu