Masar

Kotun kasar Masar ta yanke hukuncin dauri kan mata 14

Wasu mata da ke goyon bayan Mohammad Morsi na Masar
Wasu mata da ke goyon bayan Mohammad Morsi na Masar ©Reuters.

Matan su 14 ana zarginsu ne da kasancewa a cikin kungiyar Ta’adanci tare da hannu wajen tayar da boren da ake ci gaba da yi a fadin kasar.

Talla

Kotun ta kuma bayyana yadda matan suka dinga yin amfani da wukake da duwatsu a lokacin zanga zangar da aka yi a kasar jim kadan bayan tunbuke MohD Morsi daga karagar mulki.

Baya ga wadannan matan ma da akwai wasu maza shida da aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 15 saboda samunsu da laifin ingiza matan wajen aikata laifufukan da ake zargin su da aikatawa.

A cikin matan da aka daure, bakwai ‘yan shekaru kasa da 18, wadanda za a tsare su a gidan yarin da ake tsare yara kanana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.