Masar

An yi arangama tsakanin Dalibai da jami’an tsaro a Masar

Harbe-harbe a zanga-zangar Masar
Harbe-harbe a zanga-zangar Masar AFP PHOTO/MAHMOUD KHALED

‘Yan sanda a kasar Masar sun harba Hayaki mai sa Hawaye ga Dubban Dalibai masu zanga-zanga magoya bayan hambararren shugaba Muhammad Morsi a dandalin Tahrir na kasar. Masu zanga-zangar dai na nuna rashin amincewar su ne da kifar da gwamnatin ‘yan Uwa Musulmi da Soji suka yi a baya  

Talla

Zanga-zangar da aka gudanar a ranar Lahadi, ita ce ta farko da ‘ya’yan kungiyar ‘yan Uwa Musulmi suka gudanar a dandalin Tahrir wurin da aka yi boren daya hambarar da gwamnatin Shugaba Husni Mubarak, tun bayan wadda aka gudanar data kawar da gwamnatin Muhammad Morsi ran 3 ga Watan Yuli.

Masu zanga-zangar dai na furta kalaman tsinuwa da neman kawar da gwamnatin da Sojin kasar suka kafa ne, a yayinda kuma masu zanga-zanga a Dandalin Rabi’at-ladwiyya ke nuna Yatsa 4 abinda ke alamta cewar suna bayan Muhammad Morsi na jam’iyyar ‘Yan Uwa Musulmi.

A wannan Dandalin ma, a wAtan Agusta an kashe Daruruwan Mutane lokacin da jami’an tsaro suka afkawa masu zanga-zanga da suka jajircewa kashedin da aka yi masu.

Kasar Masar dai ta kasa samun kwanciyar hankali tun bayan da aka kifar da gwamnatin Muhammad Morsi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.