Najeriya

Jonathan ya mayar wa Obasanjo da martani

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Getty Images

Fadar Gwamnatin Najeriya ta mayar wa Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da martani akan wasikar suka da gazawar shugabanci da ya rubutawa Goodluck Jonathan inda kakakin gwamatin ya danganta wasikar a matsayin cin mutuncin shugaban.

Talla

Obasanjo wanda jagoranci Najeriya a Mulkin Demokuradiya tsakanin 1999 zuwa 2007 ya rubutawa Jonathan wasikar ne mai yawan shafi 18 yana mai suka da zargin Jonathan game da rashin magance matsalolin da suka shafi Najeriya da dama da suka hada da Cin hanci da Rashawa da fashin jirage da satar fetir da garkuwa da mutane.

Tuni dai fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa Obasanjo ya rubuta wa Jonathan wannan wasika, amma kamar yadda kakakin fadar gwamnatin kasar Reuben Abati ke cewa, Shugaba Goodluck Jonathan da kansa ne zai mayarwa Obasanjo da martani kan wannan batu a lokacin da ya dace.

Mai Magana da yawun shugaban kasar ya bayyana abin da tsohon shugaban kasar ya rubuta a wannan wasika da cewa babu kanshin gaskiya a ciki, sannan kuma akwai alamun munafuci a cikin saboda yadda aka bari kwafin wasikar ya fada hannun kafafen yada labarai, wanda hakan ke matsayin wani yunkuri na zubar da mutuncin shugaba Jonathan.

“Ba ni bukatar komi daga gare ka illa ka samar da ci gaba a Najeriya, amma har yanzu babu wani abu a kasa da ‘Yan Najeriya suka gani” a cewar Obasanjo a cikin wasikar da ya rubutawa Jonathan.

Obasanjo yace halin da Najeriya ta ke ciki a yanzu kamar halin da kasar ta shiga ne a zamanin mulkin Marigayi Janar Sani Abacha wanda ya kargame tsohon shugaban a gidan yari.

Obasanjo dai tamkar Uba ne ga Jonathan domin shi ya jagoranci nasarar da suka samu tare da Marigayi Ummaru Musa ‘Yar’adua a zaben 2007, kafin Jonathan ya karbi mukamin shugaban kasa bayan Yar’adua ya mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.