Masar

An cafke tsohon Firaministan Masar

Tsohon Firaministan kasar Masar Hicham Qandil
Tsohon Firaministan kasar Masar Hicham Qandil REUTER/Mohamed Abd El Ghany

‘Yan sanda a kasar Masar sun cafke tsohon Firaministan kasar a karkashin gwamnatin masu ra’ayin Islama Hisham Qandil a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da tarzoma a wasu yankunan kasar bayan harin bam da aka kai da ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 15 a garin Mansura a ranar Talata.

Talla

Kamar dai yadda majiyar ‘yan sanda ta tabbatar, an cafke Qandil ne a cikin wani yankin Saharar kasar a lokacin da ya ke kokarin tserewa zuwa kasar Sudan, kuma a can baya an taba yanke masa hukuncin dauri na tsawon shekara daya a gidan yari bayan samunsa da laifin akan sayar da hannayen jarin wani kamfani mallakar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.