Sudan-Sudan ta Kudu

Al-Bashir na Sudan ya kai ziyara Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan Omar al-Bashir ta takwaransa na Kudu Salva Kiir a fadar shugaban kasa a Juba.
Shugaban Sudan Omar al-Bashir ta takwaransa na Kudu Salva Kiir a fadar shugaban kasa a Juba. Reuters/Adriane Ohanesian

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya isa Juba babban birnin kasar Sudan ta kudu domin tattaunawa da Shugaba Salva Kiir, a daidai lokacin da dakarun gwamnatin kasar ke gwabza fada da ‘Yan tawaye masu biyayya ga Riek Machar.

Talla

Yanzu haka kuma akwai zaman tattaunawa da ake yi a Addis Ababa tsakanin wakilan bangarorin da ke fada da juna domin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Mataimakin shugaban kasa ne James Wani Igga, ya tarbi al Bashir a filin saukar jirgin sama a Juba kafin suka kama hanya zuwa fadar shugaba Salva Kiir.

Alkalumma sun ce kimanin mutane 1,000 ne suka mutu tun barkewar rikicin a ranar 15 ga watan Disemba bayan da Shugaba Kiir ya zargi Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa, zargin da ya karyata.

Wata majiyar gwamnati daga ma’aikatar harakokin wajen Sudan tace gwamnatin kasar a shirye take ta bayar da taimako domin ganin an cim ma nasara ga zaman tattaunawar da shugabannin kasashen gabacin Afrika ke jagoranta tsakanin bangarorin biyu.

A shekarar 2011 ne Sudan ta kudu ta samu ‘yancin kai bayan ta balle daga Sudan

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI