ICC-Sudan-Congo

Kotun ICC ta bukaci Congo ta cafke Al Bashir na Sudan

Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir a zauren taron kasashen Afrika karo na 22 da aka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha
Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir a zauren taron kasashen Afrika karo na 22 da aka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha REUTERS/Tiksa Negeri

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta bukaci gwamnatin kasar Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo ta cafke shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir a ziyarar da ya kai a kasar wanda Kotun ke tuhuma da aikata laifukan yaki a rikicin yankin Darfur.

Talla

Kotun ICC tace hakki ne da ya rataya akan kasar Congo ta cafke al Bashir tare da mika shi domin gurfana a gabanta.

Irin wannan kiran ne Kungiyoyin kare hakkin bil’adama irinsu Amnesty International da wasu a cikin kasar Jamhuriyyar Congo suka yi.

An dade Kotun ICC tana neman ta cafke al Bashir wanda take nema ruwa a jallo akan zarginsa da aikata laifukan yaki a rikicin Darfur a gabacin kasar Sudan, kuma shugaban ya kai ziyara ne birnin Kinsasha domin halartar taron kasashen Afrika.

Kasashen Afrika da dama dai kamar Najeriya da Chadi sun yi watsi da irin wannan kiran na Kotun a lokacin da al-Bashir ya kawo ziyara a kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.