Nijar

Manyan jami'an Areva sun gana da shugaba Issifou Mahamadou

Luc Oursel, shugaban kamfanin Areva
Luc Oursel, shugaban kamfanin Areva REUTERS/Jacky Naegelen

Shugaban kamfanin hako ma’adinin Uranium na Areva mallakin Faransa Luc Oursel, ya ce an samu muhimmin ci gaba a lokacin ganawarsu da shugaban kasar Nijar Issifou Mahamadou, wanda ya ziyarta a jiya juma’a a birnin Yamai.

Talla

Wannan ziyara dai ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnatin Nijar da kuma kamfanin domin sabunta yarjejeniyar da ke tsakaninsu, wadda wa’adin aiki da ita ya kawo karshe tun cikin watan disambar bara.

To sai dai a zantawarsa da sashen Faransanci na rfi ministan ma’adinai na kasar ta Nijar Umar Tchiana, ya ce har yanzu gwamnatin kasar na kan bakanta, na aiwatar da dokar hako ma’adinai ta kasar wadda aka kafa a shekara ta 2006, dokar da kamfanin na Areva ya ce ba zai iya yin aiki da ita ba saboda tsauraren sharudda da ke cikinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.