Nijar

Manyan jami'an Nijar sun gana da makiyan jihar Tillabery

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar
Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar France 24

Shugaban hukumar sauraron korafe-korafen ‘yan kasa a Jamhuriyar Nijar Shefou Amadou, ya gana da sarakunan gargajiya da kuma shugabannin kungiyoyin makiyaya da ke cikin jihar Tillabery kusa da iyakar kasar da Mali inda ake yawan samun tashe-tashen hankula a tsakanin al’umma.

Talla

Ziyarar ta Shefou ta zo ne mako daya bayan da kungiyoyin makiyaya da ke zaune a yankin suka gabatarwa gwamnatin kasar da wata wasika da ke zargin cewa gwamnati ta kawar da kai dangane da irin matsalolin da makiyayan ke fama da su.

Shi dai yankin kan iyakar kasar ta Mali da jamhuriyar Nijar, yanki ne da ake yawan samun hare-hare daga ‘yan bindiga, wadanda ke kashe jama’a da kuma sace dabbobin makiyayan jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.