Sudan ta Kudu

Mutanen Sudan ta Kudu suna bukatar abinci-MDD

Wasu da rikicin Sudan ta Kudu ya raba da gidajensu.
Wasu da rikicin Sudan ta Kudu ya raba da gidajensu. REUTERS/Andreea Campeanu

Majalisar Dinikin Duniya ta ce akwai bukatar a tallafawa al’ummar kasar Sudan ta Kudu da agajin gaggawa sakamakon karancin abinci mussaman a daidai wannan lokaci da damina ke karatowa, sakamakon yadda kasar ke fama da rashin hanyoyi.

Talla

A cewar John Ging wakilin hukumar jin-kai ta majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Sudan Ta kudu, akalla mutane Miliyan biyar ne ke bukatar taimako inda kuma hukumomin majalisar na fuskantar matsala a kokarinsu na kai dauki ga jama’a kafin saukar damina.

Ya kuma kara da cewar idan har damina ta sauka to hakan zai kara kawo cikas ga ayyukan jin-kai sakamakon rashin kyawon hanyoyi.

Majalisar Dinikin Duniya a baya ta kaddamar da asusun taimakawa Kasar da dala Miliyan dari tara da casa’in da tara, sai dai kuma kawo yanzu an samu rabin kudin ne kawai.

Ranar talata da ta gabata ne dai Amurka ta yi alkawarin tallafawa kasar Sudan ta Kudu da kudi dala miliyan dari hudu da goma sha daya.

Yanzu haka bangarorin biyu dake rikicin da ya jefa kasar cikin mawuyacin hali sun koma kan teburin sasantawa tun ranar talatar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.