FAO

Hukumar Abinci ta duniya zata tallafawa kasashen Afrika shida

Matsalar karancin Abinci a Jamhuriyyar Nijar
Matsalar karancin Abinci a Jamhuriyyar Nijar Janie Barrett/The Sydney Morning Herald/Fairfax Media via Getty

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta sanya hannu don bayar da tallafin kudi ga wasu kasashe shida na nahiyar Afrika, da ke fama da karancin abinci. Kasashen sun hada da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar da Habasha da Malawi da Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma kasar Sudan ta kudu. inda ko wanensu zai amfana da dalar Amruka miliyan biyu.

Talla

Sai dai Kungiyoyin kare fararen hula a Nijar suna ganin Dala Miliyan biyu sun yi kadan ga irin kasa ta Jamhuriyar Niger da ta jima tana fama da matsalar karancin abinci.

Mustafa Kadi yace Kudin sai dai ya kasance na taimako amma sun yi kadan a matsayin yarjejeniyar Tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.