Nijar

Biyan kudin fansho karshen kowane wata a jamhuriyar Nijar

Mahamadou Issoufou, shugaban jamhuriyar Nijar
Mahamadou Issoufou, shugaban jamhuriyar Nijar France 24

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani shirin kidayar tsoffin ma’aikata na kasar domin samar da sabbin alkaluma da kuma soma biyan su kudin fansho a karshen kowane wata maimakon watanni uku uku.

Talla

A jiya talata ne aka kaddamar da wannan aiki a duk fadin kasar, inda gwamnati ke cewa tana tunanin soma biyan kudin fanshon ne a karshen kowane wata domin ragewa tsoffin ma’aikatan irin waharhallun da suke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum.

Da dama daga cikin tsoffin ma’aikatan da gidan rediyo Faransa ya tattauna da su kan wannan batu, sun bayyana goyon bayansu ga shirin saboda a cewarsu yana da muhimmanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.