Nijar

Barazanar rufe kafafen yada labarai a Jamhuriyar Nijar

Zaman hukumar tace labarai a Nijar
Zaman hukumar tace labarai a Nijar

Hukumar da ke kula da kafafen yada labarai a jamhuriyar Nijar, ta ja kunnen wasu kafafen yada labarai dangane da yadda suke kaucewa doka a cikin ayyukansu.  

Talla

Daga cikin wadanda lamarin ya shafa har da gidan talabijin mallakin gwamnati kasar wato ORTN, wadda ake zargi da kin bai wa wasu bangarori na al’umma da kuma ‘yan siyasa damar bayyana ra’ayoyinsu kamar dai yadda dokokin kasar suka shata.

Har ila yau akwai wasu gidayen talabijin masu zaman kansu, da suka hada da Saraunia, Labari, Bonferey da kuma Canal 3, yayin da jaridar Opinion da ta Enqueteur masu zaman kansu da kuma wani radiyo mai suna Alternative suka shiga sahun wadanda ake zargin da yada labaran ke iya tayar da hankulan jama’a.

A cikin kwanakin da suka gabata ne dai babban darakta a ofishin Kakakin Majalisar Dokokin kasar Hama Amadou, ya gabatar da kukansa a gaban hukumar ta labarai wato CSC, yana zargin gidan talabijin na gwamnati da kauracewa ayyukan shugaban Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.